Meye ne manufar Smartdigital?

Bayan dogon nazari da tunani mai zurfi, muna kokari wajen ganin mun samar da wata dama Wanda zata taimaka wa al’ummar mu (musamman dalibai) ta fannoni da dama kamar ilimi, kimiya da fusaha.


Na kirki wani shafi a Facebook da kuma yanar gizo mai suna “Smartdigital” Wanda manufar hakan itace ingata ilimi, kimiya da fusaha bisa tsarin zamani.
Kamar yadda manufar tsarin yake, shine nuna wa al’umma mahimmancin zamanatar da ilimi, kimiya da fusaha Wanda hakan zai taimaka wajen samun sabbin dabaru Wanda za su taimaka wajen ingata rayuwar mu ta yau da kullum.
Kamar yadda abun yake a yau, duniya tana sauyawa kullum kuma ya zama dole muma mu sauya bisa yadda duniyar take tafiya.
Akwai fannoni na zamani wanda muka rasa da kuma samun Wanda za suyi mana jagora don ganin mun ci moriyar su amma cikin yaddar Allah, Smartdigital za suyi iyaka kokarin su don ganin an samu wannan damar.


Duk dacewa akwai kalubale masu yawa a gaban mu musamman yadda mutane za su rungumi wannan tsarin da kuma yadda mu ma za mu jure irin yadda za a fiskance mu, amma koma meye mamufar mu shine ace munyi nasara tare.

Da sannu za mu kawo muku tsarika Wanda za su burge Ku kuma Smartdigital na da tsarin da ba koh wani digital platform ne yake da shi ba musamman anan yankin mu na arewacin Nijeriya amma Kamar yadda mukace da sannu cikin yaddar Allah komai zai tafi daidai.
Burin mu shine Ku ba mu hadin kai, karfin gwiwa da kuma ba mu shawarwari don gina wannan tafiyar.

Mun gode!
Ali Ahmed Munkaila – CEO/Founder Smartdigital

Leave a comment

Design a site like this with WordPress.com
Get started